<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>459</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ku zo, mu tafi yaƙin nan.
 Yaƙin nan na Yesu ne.
 Kada mu koma baya fa,
 Allah yana wajenmu.

[V2]
 2) Idan mun yi musunsa,
 Al'ummai ma zo su yi.
 Ku zare takobanku fa,
 O gaba za mu yi.

[V3]
 3) Mu yi ma Allah godiya,
 Mu ce Alhamdulilahi.
 Mu dogara ga Yesu fa.
 Shi ne tutar cetonmu.

[V4]
 4) Wanda ya ƙi dogara ga Yesu
 Hallaka zai yi,
 Idan ka tuba tun yanzu
 Akwai daman gafara.

[V5]
 5) Idan ka yi shuru fa,
 Rana tana wucewa.
 Na tuba dai, zan bi Yesu,
 Yesu ne mai cetona.

[V6]
 6)Allah shi kai mu lafiya,
 Allah shi kai mu lafiya,
 Mu ce &quot;Amin&quot;, mu ce &quot;Amin&quot;.
 Mu ce &quot;Amin&quot;, mu ce &quot;Amin&quot;.</lyrics>
<title>Ku Zo, Mu Tafi Yaƙin Nan LW459</title>
</song>